Tsohon Shugaban Alkalan Najeriya Ibrahim Tanko ya rasu

Allah Ya yi wa tsohon Shugaban Alkalai na Najeriya, Mai Shari’a Ibrahim Tanko Mohammed, rasuwa.

Mai Shari’a Ibrahim Tanko Mohammed, ya rasu yana da shekara 71, kamar yadda Gwamnatin Jihar Bauchi ta tabbatar.

Rahotanni sun ce marigayin ya rasu ne a wani asibiti da ke kasar Saudiyya a ranar Talata da safe.

Kungiyar Dalibai Musulmi a Fannin Aikin Lauya ta Najeriya (NAMLAS) ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamacin.

Sanarwar da kungiyar ta fitar ta bayyana rasuwar Mai Shari’a Tanko Mohammed a matsayin  “babban rashi ga fannin aikin shari’a a Najeriya, daukacin aikin shari’ar, da al’ummar Musulmi baki daya.”

Hakazalika Gwamantin Jihar Bauchi ta bayyana rasuwar a matsayin babban rashi, tana mai addu’ar Allah Ya yi masa rahama, Ya kuma ba wa iyalansa hakurin jure wannan rashi.

Post masu alaƙa

Rundunar yan jihar Kano ta kama mutane 3 da zargin fashi da makami da garkuwa da cin zarafin mace a Rogo.

INEC ta faɗi rumfunan da za ta yi gwajin zaɓen shugaban ƙasa

Ina tsaka da yin aski aka ɗauke ruwa a Villa – Tinubu