Ganduje ya janye shirin kafa sabuwar Hisbah a Kano

Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da janye yunƙurinsa na kafa rundunar ƴan sakai da ya kira da Hisba Fisabilillah.

A wata sanarwa da shugaban kwmaitin na kafa Hisba a Kano ƙarƙashin Ganduje, Baffa Babba Ɗan Agundi ya fitar ranar Talata, Ganduje ya ce janyewar ta faru ne bayan ganawa da masu ruwa da tsaki daga ƙananan hukumomin jihar guda 44 na jihar.

.Sanarwar ta ce an yanke shawarar sauya matsayar ne sakamakon martani da jama’a suka yi ta yi da kuma damuwa da ruɗu da al’amari ya janyo.

‘’Masu ruwa da tsakin sun cimma matsayar cewa mun fasa kafa rundunar domin bai wa gwamnatin jiha ta waiwayi korar ma’aikan Hisba da ta yi ta kuma warware matsalar ta hanyar tattaunawa,” in ji sanarwar.

Post masu alaƙa

AIG Garba Ahmed ya bukaci daliban Sakandaren ’Yan Sanda Dawakin Kudu su zama jakadu na gari.

Babu ɗaga ƙafa tsakanin mu da masu sha da dillancin miyagun ƙwayoyi a Kano – Anti-Phone Snatching Force.

Kwamitin yaki da shaye-shaye da fadan daba na Kano ya nemi hadin kan hukumomin tsaro