Najeriya ta samu gibin tiriliyan 30 a kuɗin shigar da ta yi hasashen samu a 2025 – Minista

Ministan Kuɗi Wale Edun, ya bayyana a ranar Talata cewa Gwamnatin Tarayya ta yi asarar kuɗaɗen shiga mai yawa a shekarar kuɗi ta 2025.

Ya ce duk da cewa gwamnati ta yi hasashen samun Naira tiriliyan 40.8 a wannan shekara, abin da ta samu gaba ɗaya bai wuce Naira tiriliyan 10.7 ba.

Edun ya yi wannan bayani ne a gaban kwamitocin Majalisar Wakilai kan Kuɗi da Tsare-tsaren Ƙasa yayin zaman tattaunawa kan Matsakaicin Tsarin Kasafin Kuɗi (2026–2028).

Ya tuna cewa gwamnati ta yi hasashen samun Naira tiriliyan 40.8 a 2025 domin tallafawa kasafin kuɗin Naira tiriliyan 54.9 da aka kira “kasafin dawowa da daidaito,” wanda aka tsara don daidaita tattalin arziki, tabbatar da zaman lafiya da kuma shimfiɗa tubalin ci gaba na dogon lokaci.

Sai dai, ministan ya ce a halin da ake ciki, jimillar kuɗaɗen shiga na shekarar 2025 na iya karewa a kusan Naira tiriliyan 10.7.

A cewarsa, wannan gibin ya samo asali ne daga raunin kudaden shiga daga man fetur da iskar gas, musamman harajin ribar man fetur da harajin kamfanoni daga kamfanonin mai da gas, tare da rashin inganci a wasu sassan kudaden shiga.

“A halin da ake ciki, kudaden shiga na tarayya na shekarar gaba ɗaya za su kare a kusan Naira tiriliyan 10.7 idan aka kwatanta da hasashen Naira tiriliyan 40.8,” in ji Edun ga ’yan majalisa.

Bayanan ministan dai sun bambanta da furucin Shugaba Bola Tinubu a watan Satumba, inda ya ce gwamnati ta riga ta cimma burin kudaden shiga.

“Yau zan iya tsayawa a gabanku in yi alfahari: Najeriya ba ta aro kuɗi. Mun cimma burin kudaden shiga na wannan shekara tun a watan Agusta,” in ji Tinubu ga mambobin ƙungiyar The Buhari Organisation da suka kai masa ziyara a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Sai dai a ranar Talata, Ministan Kuɗi ya amince cewa gibin kudaden shiga ya shafi aiwatar da kasafin kuɗin Naira tiriliyan 54.9 na 2025.

Ya bayyana cewa duk da gwamnati ta tara kusan Naira tiriliyan 14.1 ta hanyar aro, haɗin kuɗaɗen shiga bai kai abin da ake buƙata ba don cike kasafin kuɗin shekarar.

Sai dai duk da gibin kudaden shigar, Edun ya ce gwamnati ta ci gaba da biyan muhimman bukatu ta hanyar abin da ya kira daidaita sarrafa kudaden baitul-malinta.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda