Masana kiwon lafiya sun bayyana cewa cutar hawan jini da suga na cikin cututtukan da ke haddasa ciwon koda – ya kamata mutum ya dinga kokarin zuwa asibiti don a ba shi magungunan da suka dace da kuma kula da ciwonsa na hawan jini ko ciwon sukari don kare kaii daga kamuwa da ciwon koda. […]
Tsohon sakataren kungiyar yan jarida na kasa ( NUJ) Chief Jola Ogunlusi, yam utu yana da shekaru 91 a duniya kamar yadda iyalansa suka tabbatar a ranar Asabar a Jihar Legos. Kar Ku Bari Akidun Siyasa Su Hana Ku Zaman Lafiya A Kano : Kashim Shattima Jami’an Tsaron Kasa Da Kasa Sun Dawo Nnayereugo Nijerisa […]
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya shawarci Kanawa kan kada su bari bambance-bambancen aƙidu na siyasa su zama silar hana su zaman lafiya da haɗin kai. Ya faɗi hakan ne a jawabinsa lokacin da ya je yi wa Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, ta’aziyar rasuwar mahaifinsa — Galadiman Kano, Abbas Sunusi. Shettima ya jaddada […]
Rundunar yan sandan Nijeriya ta tabbatar da cewa, jami’an tsaron kasa da kasa na Interpol, sun dawo da matashin nan mai suna, Benjamin Best Nnayereugo, wanda akafi sani da Kilaboi daga kasar Qatar bisa zarginsa da halaka wata budurwarsa bayan sun samu sabani a gidansa dake jihar Legos. Kakakin rundunar yan sandan Nijeriya, ACP Olumuyiwa […]
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshen jihar Kano ta gina wajen gyaran tarbiyar wadanda suka fada harkar shaye-shaye a jihar.
Wasu yan bindiga da ba a san ko suwaye ba, sun sace wani dan kasar chaina mai suna Yangi Ming, a birnin tarayya Abuja, inda suka nemi kudin fansar naira miliyan 300. Rahotanni na cewa ,Yangi, yana aiki ne babban kantin Panda Supermarket, kuma an sace shi da misalin karfe 5pm sanye da gajeren wando […]
Da safiyar jiya Laraba ne dai aka ga jarumar tiktok Rahama Sa’idu na bayyana cewa an karya mata allon da ke gaban shagonta, kuma ta sha alwashin sai an biyata.
Gwamnatin Jihar Kano ta umarci yan kasuwar mangoro dake na’ibawa yanlemo dasu kauracewa yin bahaya a Wani kebantaccen fili dake bakin titi Kuma su daina sauke Kaya a kusa da wajen domin kaucewa kamuwa da cututtikan da iska kan Iya yadawa. Kwamishinan ma’aikatar Muhalli da kula da sauyin yanayin na Jihar Kano Dr. Dahiru […]
An naɗa mace ta farko a matsayin mai magana da yawun rundunar sojin ƙasa ta Nijeriya. Appolonia Anaele mai muƙamin Laftanar Kanar ce za ta karɓi muƙamin daga hannun Manjo-Janar Onyema Nwachukwu. Bayanai sun ce muƙamin nata zai fara ne a ranar Talata 22, ga watan Afrilun da muke ciki. Shekaru sama da 50 ke […]