NDLEA TA Gina Gidan Gyaran Tarbiyyar ‘Yan Shaye-shaye A Kano

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshen jihar Kano ta gina wajen gyaran tarbiyar wadanda suka fada harkar shaye-shaye a jihar.

Shugaban hukumar na kasa, Janar Buba Marwa Mai Ritaya ne ya kaddamar da wajen gyaran tarbiyar wadanda suka fada harkar shaye-shaye da gidajen kwana na jami’an hukumar.

Yayin kaddamar da gidajen, Marwa ya ce jihar Kano ce ta biyu, a mafi yawan masu Shan kayan maye a fadin Nageria.

Janar Marwa ya ce za su yi magana da Gwamnatin jihar Kano don ta basu babban filin da zata kara Gina bariki don yaki da Shan kayan maye.

Shugaban ya kuma musanta   Zargin rashin kayan aiki da hukumar take fama dashi, Inda ya ce Gwamnatin tarayya tana iya bakin Kokarin ta domin samar da motocin aiki.

A karshe ya yi kira ga iyaye da su ci gaba da sanya Ido kan ‘ya’yansu tare daukar mataki a duk lokacin da suka ga sauyi atattare da su.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda