Masu Garkuwa Sun Nemi Kudin Fansa 300m Kafin Su Saki Dan Kasar Chaina Da Suka Sace A Abuja

Wasu yan bindiga da ba a san ko suwaye ba, sun sace wani dan kasar chaina mai suna Yangi Ming, a birnin tarayya Abuja, inda suka nemi kudin fansar naira miliyan 300.

Rahotanni na cewa ,Yangi, yana aiki ne babban kantin Panda Supermarket, kuma an sace shi da misalin karfe 5pm sanye da gajeren wando mai launin ruwan kasa da bakar riga a yankin Durimi Abuja.

Wata yar uwarsa mai suna, A’isha Pan, mazauniyar Sharada Kano, ita ce ta samu kiran masu garkuwar da mutanen inda suka bukaci a biyasu naira miliyan 300 kafin su sake shi.

Kawo yanzu dai rundunar yan sandan birnin tarayya abuja , bata ce komai ba kan wannan lamari.

Post masu alaƙa

AIG Garba Ahmed ya karrama sabon kwamishinan yan sanda CP Taiwo a Kano.

Yan sandan Kano sun miƙa wa masu su motoci biyu da suka ƙwato tare da kama mutum Daya da ake zargi.

Bene mai hawa daya da ake ginawa ya rushe a jihar Sokoto