Cibiyar Kasafin kudi Lafiya ta Afirka (AHBN) a Nijeriya ta jaddada bukatar ƙara ba da kuɗi da kuma sakin kuɗi da wuri don shirye-shiryen alluran riga kafi a Jihar Kano.
Dr. Musa Muhammad Bello, Wakilin AHBN na Jihar Kano , ya yi wannan kira yayin wani taron manema labarai da rarraba katin sakamako a Asibitin Muhammad Abdullahi Wase (wanda aka fi sani da Asibitin Nasarawa) .
Dr. Musa Muhammad Bello ya bayyana cewa Cibiyar Kasafin kudin Lafiya ta Afirka (AHBN) tana gudanar da wannan aikin tare da haɗin gwiwar Cibiyar Nazarin Cututtuka ta Afirka (AFENET) da tallafin Ƙungiyar da ke ba da tallafi don inganta allurar riga kafi a duniya GAVI. tare da hadin gwaiwar haɗin gwiwar Hukumar Kula da Kiwon Lafiya a matakin Farko ta Ƙasa (NPHCDA),da ma’aikatar kula da lafiya a matakin farko na jihar kano.
Makasudi ayyukan shine don haɓaka ilimin ƙwararrun kiwon lafiya game da ayyukan rigakafi da haɓaka buƙatun rigakafi don isa ga yaran da ba a kai garesu ba a jihohi huɗu, waɗanda suka haɗa da Kano, Sokoto, Bauchi, da Borno.
Dokta Musa Muhammad Bello ya bayyana cewa, aikin na ZDLH yana neman magance gibin da ke tattare da daidaiton rigakafi ta hanyar samar da tsari mai tsauri ga Najeriya don inganta amfani da bayanai da kuma samar da shaida cikin gaggawa don ganowa, aunawa, sa ido, da kuma kai ga yaran da basu samu rigakafi ba, da kuma adadin da aka rasa.
domin tabbatarwa kowani yaro ya samu riga kafin,da Magance gibin da ke tattare da rashin daidaiton alluran rigakafi da kokarin ganin an raraki wannan cuta ta polio da ga Afrika.
ya kara da cewa, “Ayyuka da dama na tsarin kasafin kudin Afirka (AHBN) sun gudanar da ayyuka da yawa a karkashin wannan aiki sama da shekaru biyu, ciki har da kafa kungiyar al’umma don bayar da shawarwari da masu ruwa da tsaki, gudanar da sa ido kan alluran rigakafi tare da hadin gwiwar AFENET, a kananan hukumomin Kumbotso da Sumaila tare da bunkasa tsarin bin diddigin kasafin kudin rigakafin rigakafin da kuma tantance katin tantancewa,” in ji Musa.
DR musa ya godewa gwamanatin jihar kano da kokarin da takeyi a bangaren lafiya sannan yayi kira ga gwamnatin da ta kara kokari gurin tabbatar ana sakar kudin da ya kamata a fitar na harkokin lafiya da wuri domin tafida aikin yadda ya kamata.
Dr. Bello ya bayyana cewa sakin kuɗi na alluran riga kafi da wuri yana da muhimmanci don:
✔ Ingantaccen isar da alluran riga kafi
✔ Kyakkyawan sakamako na lafiyar jama’a
✔ Tabbatar da cewa alluran suna samuwa ga mutanen da ya dace.