Tsohon Kwamishinan Yan Sandan Kano CP Sama’ila  Dikko Ya Ce Boye Laifin Yaya Ne Ke Rura Rikicin Fadan Daba.

Tsohon kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya bayyana cewa iyaye suna da matukar gudunmawar da za su bayar domin tabbatar da dakile matsalar fadan daba dake fuskantar al’ummar jihar Kano a halin yanzu.

Sama’ila Dikko, ya bayyana hakan ne a daren jiya talata, yayin tattaunarwasa da MUHASA TV da Radio ta wayar tarho.

Ya ce wajibi ne iyaye susan inda yaransu suke zuwa da wadanda suke mu’amula , sannan su tabbatar basa cikin harkar shan miyagun kwayoyi da kuma hana su yin yawace-yawacen da su dace ba.

Ya kara da cewa idan aka yi hakan za a samu hanya mai kyau wajen dakile wannan al’amari da yake fuskantar mu a halin yanzu.

Tsohon kwamishinan ya ce wasu daga cikin iyaye ne suke boye laifukan da yayansu suke aikatawa, musamman rashin bayar da hadin kai ga jami’an tsaro, don su samu karfin gwiwar kama su a gurfanar dasu a gaban kotuna bayan kammala bincike.

CP Dikko ya rike kwamishinan yan sandan Kano daga watan Fabarairun 2021 zuwa watan Yulin 2022, inda yayi ritaya daga aikin dan sanda sakamakon cika shekaru 60 da yayi .

Haka zalika ya bayyana muhimmancin da kotuna suke dashi wajen hukunta wadanda aka samu da aikata laifukan cikin gaskiya da adalci.

Sai dai ya ce idan ana yin hukunci ba tare da son kai ba , ko ware wasu ba , za a magance matsalar cikin Ruwan sanni, amma idan ana hukunta iya wadanda basu da gata to ba za a samu saukin wannan matsalar ba.

‘’ Wadannan yara suna da kungiya ne idan suka aikata laifi iyayensu basa iya sani, wadannan abokan harkar tasu , sune za su shiga wani dattako suje su nemi belinsu, soboda haka duk wanda ya zo neman belinsu shima akamashi a gurfanar da shi a gaban kotu’’.

Ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro musamman yan sanda su daina bayar da beli ga wadanda basu da dangantaka ko alaka da wadanda ake zargi da aikata wani laifi , inda ya ce suma aka masu a gurfanar dasu a gaban kotu.

A karshe ya ce yakamata adaina bayar da belin irin wadannan yara kawai a dinga gurfanar dasu a gaban kotu don su fukanci hukunci.

Post masu alaƙa

Ƙungiyar muhaɗu mugyara ta bayyana Muhasa TVR a matsayin kan gaba wajen gyaran tarbiyyar al’umma.

Fursuna ya tsere bayan hatsarin motar jami’ai a Yobe

Katsina ta kafa kotunan tafi da gidan ka don gaggauta hukunta ’yan ta’adda