Home » Cibiyar Yaƙi Da Ta’addanci Ta Miƙa Janar Tsiga Da Wasu Ga NSA

Cibiyar Yaƙi Da Ta’addanci Ta Miƙa Janar Tsiga Da Wasu Ga NSA

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

Cibiyar yaƙi da ta’addanci ta ƙasa (NCTC) ta miƙa tsohon Darakta-Janar na masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), Birgediya Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya) ga mai ba shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu.

Tsiga, wanda aka kuɓutar bayan ya kwashe kwanaki 56 a tsare, a ranar Laraba an miƙa shi ne tare da wani tsohon Ambasada da sauran waɗanda ’yan ta’addan suka yi garkuwa da su.

Aminiya ta ruwaito yadda aka yi garkuwa da tsohon shugaban Hukumar NYSC daga mahaifarsa a ƙaramar hukumar Bakori ta Jihar Katsina, a ranar 5 ga Fabrairu, 202

Da yake jawabi gabanin miƙa su a hukumance, Shugaban Cibiyar NCTC, Manjo-Janar Adamu Laka, ya bayyana cewa jami’an tsaro daga sojoji, jami’an DSS, ’yan sanda da sauran hukumomin sun yi aiki ba dare ba rana domin ganin an ceto su.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?