Rundunar yan jihar Kano ta kama mutane 3 da zargin fashi da makami da garkuwa da cin zarafin mace a Rogo.

Rundunar yan jihar Kano sun kama mutane 3 kan fashin da makami da garkuwa da mutane a Rogo.

 

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama mutane uku bisa zargin shiga gida ba da izini ba da cin zarafin matar gida da fashi da makami da kuma garkuwa da mutane a ƙaramar hukumar Rogo.

 

Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 23 ga Nuwamban 2026, inda ya ce lamarin ya faru ne a ranar 3 ga Nuwamba da misalin ƙarfe biyu na rana a ƙauyen Aleko da ke ƙaramar hukumar Rogo.

 

Ya ce waɗanda ake zargin sun kutsa cikin gidan wani mazaunin ƙauyen ɗauke da makamai, inda suka farmaki mutanen gidan, suka ci zarafin wata mata, sannan suka sace babur ƙirar Boxer mai launin ja, wanda darajarsa ta kai Naira miliyan ɗaya da dubu 150, da kuma buhunan barkono busassu 25 da aka ƙiyasta kuɗinsu ya kai Naira dubu 850.

 

Sanarwar ta ce mai gidan ya gane ɗaya daga cikin maharan mai suna Nafi’u Lawal, wanda aka fi sani da Gamji, lamarin da ya taimaka wa jami’an rundunar sashen yaƙi da garkuwa da mutane wajen gudanar da bincike da cafke waɗanda ake zargin.

 

Mutanen da aka kama sun haɗa da Nafi’u Lawal, mai shekaru 21, mazaunin Aleko; Auwalu Shafi’u, mai shekaru 26, wanda aka fi sani da Bakin Tuwo, wanda aka kama a ƙaramar hukumar Doguwa; da Yunusa Sale, mai shekaru 26, wanda aka fi sani da Bammi, mazaunin ƙauyen Jajaye a Rogo.

 

CSP Kiyawa ya ce yayin bincike, waɗanda ake zargin sun amsa aikata laifin, tare da bayyana hannu a wasu hare-haren garkuwa da mutane biyu, ciki har da na Ibrahim Iro, wanda aka fi sani da Dangi, da Shadari, wanda ake kira Ardo, dukkaninsu mazauna Aleko ne

 

Ya ƙara da cewa waɗanda ake zargin sun bayyana cewa an saki mutanen ne bayan an biya kuɗin fansa na Naira dubu 900 ga ɗaya daga cikinsu sannan kuma aka biya Naira miliyan ɗaya ga sauran mutumin.

Kwamishinan ’yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa jami’an sashen yaƙi da garkuwa da mutane bisa ƙwarewa da gaggawar gudanar da aikin da ya kai ga cafke waɗanda ake zargin.

Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike domin cafke sauran waɗanda ake zargi da hannu a laifukan, da kuma gano kayayyakin da aka sace, kafin gurfanar da waɗanda aka kama a gaban kotu.

Ta kuma buƙaci al’umma su ci gaba da ba jami’an tsaro sahihan bayanai, tare da kai rahoton duk wani motsi ko mutum da suke zargi zuwa ofishin ’yan sanda mafi kusa ko ta lambobin gaggawa: 08032419754, 08123821575 da 09029292826.

Post masu alaƙa

INEC ta faɗi rumfunan da za ta yi gwajin zaɓen shugaban ƙasa

Ina tsaka da yin aski aka ɗauke ruwa a Villa – Tinubu

Adadin waɗanda suka mutu a hatsarin kwale-kwalen Bayelsa ya kai 29