Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya kai ziyarar duba halin tsaro da ganawa da al’umma a yankin Tudun Wada domin karfafa hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da jama’a.
Ya ce ziyarar ta bashi damar samun bayanai kai tsaye kan halin tsaro a kananan hukumomin, Tudun Wada da Doguwa da Sumaila da Kiru, tare da nemo hanyoyin magance matsalolin tsaro.
Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar talata.
Haka kuma ya yabawa al’umma bisa hadin kai da bayar da sahihan bayanai ga jami’an tsaro, yana mai kira gare su da su rika kai rahoton duk wani abu da ake zargi ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa.
Kwamishinan ya kuma yabawa yan sandan bisa kokarinsu wajen yaki da laifuka, tare da umartarsu da su ci gaba da aiki cikin kwarewa da gaskiya da kuma mutunta hakkin jama’, su guji cin hanci da rashawa, kuma su rika gaggauta amsa kiran gaggawa daga jama’a .
A nasa jawabin, Hakimin Tudun Wada kuma Katikan Kano, Alhaji Habibu Bello, ya yaba da ziyarar tare da bukatar jama’a su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai domin tabbatar da zaman lafiya.
Shi ma Ibrahim Ali Fulatan ya tabbatar da ci gaba da hadin kai tsakanin kwamitocin tsaro na al’umma da jami’an ‘yan sanda.
Taron ya samu halartar shugabannin gargajiya da na addini da jami’an tsaro da kungiyoyin al’umma daban-daban, sannan ya kare da tattaunawa kan matsalolin tsaro da hanyoyin magance su.
