Cutar mashaƙo ko kuma Diphtheria a Turance ta sake yin ajalin mutum ɗaya a Najeriya, kamar yadda rahoton hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ya nuna.
Sabon rahoton na NCDC da ta wallafa a yau Asabar ya nuna mutumin ya rasu ne a tsakanin 16 ga watan nan zuwa yau. Sai dai ba ta faɗi jinsi ko suna ko jihar da mamacin ya fito ba.
Jimillar mutum 16 aka yi zargin sun kamu da cutar a jihohi biyu tun daga 16 ga watan Maris, amma uku ne aka samu tabbacin suna ɗauke da ita.
- An Kama ‘Yan Daba 12 Kan Zargin Kashe Matashi A Masallaci A Kaduna
- Kananan Yara Sama Da Miliyan 1 Za Su Rasa Tallafin USAID
Jimillar mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar tun daga shekarar 2022 sun zama 42,805 a jihohi 26 na ƙasar. Daga cikinsu 1,331 sun mutu.
NCDC ta ce yara ‘yan ƙasa da shekara 14 ne suka fi kamuwa da cutar. kamar yadda kafar yada labarai ta BBC Hausa ta wallafa.