Hisbah za ta fara farautar masu aikata baɗala a Kano

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ce, za ta fara tsauraran matakan daƙile ayyukan da ba su dace ba a faɗin jihar ƙarƙashin sabon shirin “Operation Kano First”.

Mataimakin Kwamandan Janar na Hukumar, Mujahid Aminuddeen ne ya bayyana hakan bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bai wa Hisbah motoci 10 da babura 50 domin ƙarfafa ayyukanta.

Ya ce, jami’an Hisbah sun fara sintiri a wasu manyan hanyoyin Kano, kuma za su ci gaba da sintiri domin wayar da kan jama’a da kuma ɗaukar mataki kan waɗanda suka karya doka.

“Duk wanda aka kama yana aikata irin waɗannan abubuwan za a kama shi, kuma zai fuskanci hukunci.”

Hisbah ta ce, sababbin motocin da baburan za su taimaka wajen ƙara yawan sintirin jami’an hukumar da kuma kai ɗauki cikin gaggawa ga ƙorafe-ƙorafen jama’a.

Post masu alaƙa

INEC ta kai wa CBN ajiyar muhimman kayan zaɓen Gwamnan Osun

Rundunar yan sandan shiyya ta daya ta kama Mutane biyar kan zargin jabun magunguna da sojan Gona.

Kwalejin sojan ruwa dake Dawakin-Tofa ta kara karfafa hadin gwiwar aiki tare da rundunar yan sandan Kano.