• Home  
  • Dakarun gwamnatin kasar Sudan da ta RSF sun kulla yarjejeniyar tsagaita wuta saboda babbar sallah
- Kasashen Ketare - Labarai

Dakarun gwamnatin kasar Sudan da ta RSF sun kulla yarjejeniyar tsagaita wuta saboda babbar sallah

A yau ne yarjejeniyar tsagaita wuta da shugaban rundunar dakarun RSF ya sanar za ta fara aiki domin bukukuwan babbar sallar Idi da za a fara ranar Laraba.

An bayar da sanarwar dakatar da rikicin ne a wani sakon murya da aka watsa a gidan talabijin, wanda shugaban kungiyar RSF, Muhammad Hamdan Dagalo, ya gabatar.

Ya ce matakin zai yi aiki ne a ranakun Talata da Laraba.

Janar Hemedti ya kuma yi Allah-wadai da cin zarafi da ake yi wa fararen hula – ciki har da wadanda sojojinsa ke yi.

Ana zargin kungiyar ta RSF da aikata laifukan cin zarafin mutane a Darfur.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000