Rundunar ‘Yan sandan Najeriya ta sanar da shirin janye wasu jami’an ‘yan sandan da ke ba da kariya da kuma rakiya ga manyan mutane da nufin sake tura su aiki a kan tsaron kasa.
Sabon Sufeto-Janar ɗin ‘Yan Sandan Najeriya, Olukayode Egbetokun, ya ce, “Duk da cewa kare martabar manyan mutane ya kasance mafi muhimmanci, amma ya zama wajibi mu daidaita abubuwan da muka sa a gaba don magance matsalar tsaro da ke addabar al’ummar ƙasar baki ɗaya.
A farkon watan nan ne dai shugaba Bola Tinubu ya yi sauye-sauye a jami’an tsaron Najeriya inda ya nada sabbin kwamandojin jami’an tsaro da suka hada na rundunar sojin ƙasar baki ɗaya.