Sufeton janar ɗin ‘yan sandan Najeriya Kayode Egbetokun ya ce za su bai wa masu zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa kariya a ƙasar.
Sufeto janar Kayode Egbetokun ya ce “za mu kare masu zanga-zanga matuƙar dai ta lumana ce”.
A wani bayani da ya yi jim kaɗan bayan wata muhimmiyar ganawa da manyan jami’an rundunar na faɗin Najeriya, sufeto janar ɗin ya yi kira ga matasa da su haƙura da zanga-zangar domin a cewarsa “gwamnati na bakin ƙoƙarinta”.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai kan bada kariya ga masu zanga-zanga, tun da haƙƙin ‘yan ƙasa ne su bayyana rashin gamsuwarsu da wasu al’amuracikin lumana, BBC Hausa ta ruwaito cewa, babban sufeton ‘yan sandan Najeriyar ya ce,
“Idan zanga-zangar ta lumana ce za ku ganmu muna kare masu yinta. Lallai ba za mu yi adawa da zanga-zangar lumana ba, za mu taimaka wa masu zanga-zangar lumana saboda ‘yancinsu ne”
“Amma kuma akwai alhaki a kanmu na kare rayuka da dukiyoyi. Ba za mu zauna muna kallon ‘yan daba suna ƙona gine-gine da sunan zanga-zanga ba, ba za mu yarda da wannan ba.”
- Dambarwar Matatar Man Dangote Babbar Matsalace-Atiku Abubakar
- Ɗangote Zai Fara Shigo Da Ɗanyen Mai Daga Libiya
Sufeton ‘yan sandan Najeriyar ya ce, sun samu rahotannin sirri da ke cewa akwai wasu da ke kiran matasa su kwaikwayi irin zanga-zangar da mutanen Kenya suka yi a Najeriya “kai da kai”.
“Ina amfani da wannan damar in yi kira ga matasan Najeriya, don Allah ku yi watsi da duk wani kira na neman ku fito ku tayar da hankali. Najeriya ta taɓa samun kanta a cikin matsalolin mummunar zanga-zanga.”
A nasa ɓangaren, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci masu shirya zanga-zangar “su dakata tukunna, har sai sun ji irin martaninsa game da koke-kokensu”.
Shima dai tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar ya ce abin mamaki ne yadda waɗanda suka jagoranci zanga-zanga a 2012 ke adawa ƙiri-ƙiri da wadda ake ƙoƙarin shiryawa a 2024.