Attajirin da ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afirka, Aliko Dangote, ya gana da shugabar ƙasar Tanzaniya Samia Suluhu, inda ya yi alƙawarin cewa za a fara gina matatar mai a yankin gabashin Afirka a wannan shekara.
Shugaba Samia ta tattauna da Dangote ne a fadar gwamnatin ƙasar da ke Dar es Salaam a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan yankin da za a gina matatar man ta kimanin dala biliyan 17.
Dan kasuwar na Najeriya ya ce tawagar ƙwararru za ta ba da shawara kan wurin da ya dace da matatar man a gabashin Afirka, inda ya ƙara da cewa har yanzu akwai buƙatar a yi la’akari da wasu abubuwa kafin a yanke hukunci na ƙarshe.
“Kamar a Najeriya, ba mu gina matatar kawai a inda mai yake ba, mun gina ta ne a inda yanzu za a iya samun nau’ikan ɗanyen mai daban-daban, ba wai a dogara kan wani danyen mai iri guda ba,” in ji shi.
Shugaban ƙasar Kenya William Ruto dai ya bayar da shawarar gina matatar man birnin Tanga dake arewacin Tanzaniya, amma Dangote ya bayyana sha’awarsa ta gina matatar a birnin Mombasa na ƙasar Kenya.
Dan kasuwar ya ce ana sa ran matatar man za ta riƙa sarrafa ganga 650,000 a kowace rana.