Daga: Shareep Khaleepha Sharifai
Direbobin manyan motocin dakon kaya da ke jigila daga Arewaci zuwa yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, sun gudanar da wani gangami inda suke zargin ƴan awaren Biafra da kai musu hare-hare tare da ɗora musu tara mai dimbin yawa.
Direbobin sun yi ƙorafin cewa ɓata-garin a yankin kudu maso gabashin ƙasar, sun kashe ƴan uwansu da dama tare da ƙona kayan da suka dauko da ma ɗaruruwan motocin.
Galibin ƙorafe-ƙorafen da direbobin manyan motoci ke yi sun haɗa da cin zarafi da suke fuskanta.
Hassan Shittu wanda shi ne shugaban ƙungiyar manyan motoci dakon kaya na shiyyar arewa ya shaidawa BBC cewa sun shafe fiye da shekara takwas suna fuskantar cin zarafi daga ƴan awaren Biafra da wasu bata-gari muddin suka lura cewa sun fito ne daga yankin arewa.
- Ma’aikatan Hukumar Samar Da Ruwa Ta Jihar Kano Sun Janye Yajin Aiki
- Birgediya Janar Kunle Nafiu Ya Zama Shugaban NYSC
” Wallahi tamkar kamar mu ba ƴan Najeriya mutanen nan suke ɗaukar mu ba. In ka zo Enugu za ka biya jangali, in ka zo Imo za ka biya jangali, haka ma a Abia”
” Akwai wani gari da ke kusa da Umuahia, gaskiya ba bu tsaro a wurin, kana tsaya wa ka na pakin wani bata-gari zai zo ya tsare ka, kafin ka tsaya zai fara dukan motarka”, in ji shi
Shugaban ƙungiyar direbobin manyan motocin ya ce ƙabilanci na cikin dalilan da suka sa ake kai mu su hari.
” Gaskiya akwai ƙabilanci a ciki, ko kirista ne in dai ɗan arewa ne, in dai za ka yi hausa, to su ba ruwansu”
Direbobin dai sun yi kira ga mahukuntan ƙasar da su inganta tsaro a hanyar Enugu zuwa Aba da birnin Fatakwal.
Mohamed Jos wanda ya halarci gangamin da direbobin suka yi ya ce ya zama wajibi ga gwamnatin tarraya ta sa baki a cikin alamarin.
”Suna kira ga gwamanti ta sa ido, ta sa baki, ta sa tsaro, a daina kashe mu su mutane a kan hanya”
”Sun fadi cewa a shekara takwas kaɗai an kashe mu su direbobi guda hamsin, wasu gawarwakin an iya gani, yayin da wasu ba’a iya gani ba”, in ji shi
Ya ce shi yasa suke ganin abin ya ishe su kuma in bai yiwu ba ‘za su daina tafiyar kwata-kwata’
Direbbobin sun ce sun rubuta wasiƙa ga ofishin babban sufeton ƴansandan ƙasar inda suka gabatar da kokensu.
Haka kuma direbobbin sun yi iƙirarin cewa an kashe mu su direbobin 20 tsakanin watan janairu da disambar bara a wasu yankunan jihar Imo.