• Home  
  • Shugaba Tinubu Ya Bada Umurnin Kammala Titin Abuja Zuwa Kano
- Babban Labari - Labarai

Shugaba Tinubu Ya Bada Umurnin Kammala Titin Abuja Zuwa Kano

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin kammala aikin babbar hanyar Abuja zuwa Kano cikin wata 12 masu zuwa kamar Yadda Mai magana da yawun fadar shugaban Sunday Dare, ya sanar.

Daga: Safiyanu Haruna Kutama

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin kammala aikin babbar hanyar Abuja zuwa Kano cikin wata 12 masu zuwa kamar Yadda Mai magana da yawun fadar shugaban Sunday Dare, ya sanar.

A cewar sa, Shugaba Tinubu ya amince da kasafin kammala wuraren da ba a gama ba a kan titin Abuja-Kaduna, da na Kaduna-Zaria cikin wata 12,” kamar yadda ya wallafa a shafinsa na dandalin X.

A watan Janairu gwamnatin Bola Tinubu ta sanar da bai wa wani sabon kamfani ƙarashen aikin titin bayan ta ƙwace kwangilarsa daga hannun Julius Berger.

Wasu dai na ganin akwai lauje cikin nadi game da Yadda ake tafiyar da aikin hanyar idan aka kwatanta sauran muhimman hanyoyi da ake aikinsu a wasu yankunan kasar nan.

Wasu kuma na ganin akwai sakacin wasu yan majalisun yankin ta yadda suka gaza yin magana da murya daya akan wadannan muhimman ayyuka da zasu karfafa tattalin arzikin yankin Arewacin kasar Najeriya.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai