Ma’aikatan Hukumar Samar Da Ruwa Ta Jihar Kano Sun Janye Yajin Aiki

Daga: Safiyanu Haruna Kutama

Ma’aikatan hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano sun janye yajin aikin da suka shiga a ranar 26 ga watan Fabrairun 2025, akan rashin fara biyansu sabon tsarin mafi ƙarancin albashi.

Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta jihar Kano, reshen hukumar samar da ruwan sha a jihar Kwamared Najib Abdulsalam ne ya shaidawa jaridar voice of Afric VOA, hakan a cikin daren yau Litinin, ya ce sun janye yajin aikin ne sakamakon zaman tattaunawar da suka yi da ɓangarorin da lamarin su ya shafa.

“Daga cikin waɗanda muka yi zaman tattaunawar da su akwai Kwamishinan Kasafi da tsare-tsare na jihar Kano, da shugaban ƙungiyar ƙwadago na jihar NLC, Kwamared Kabiru Inuwa, da babban sakatare guda biyu da kuma wasu masu bai wa gwamnan Kano shawara guda biyu, wanda gwamnan ya naɗa domin zama da ma’aikatan, “in ji Kwamared Najib”.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ma’aikatan hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano, ta tsunduma yajin aikin ne daga ranar 26 ga watan Fabrairun 2025, bisa rashin sanya su a sabon tsarin mafi ƙarancin albashi, wanda gwamnatin Kano ta fasa biyan ma’aikata kusan watanni huɗu a jihar.

Kwamared Najib ya kuma ce bisa janye yajin aikin da suka yi ne suke umartar dukkanin ma’aikatan hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano, da su koma bakin aikin su daga gobe Talata 04 ga watan Maris na shekarar 2025.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *