Kasurgumin dan ta’adda Kachallah Bello Turji, ya jaddada cewa karamin ministan tsaro na yanzu Bello Matawalle tallafawa ta’addanci a yankin Arewa maso Yamma.
A cikin wani sabon faifan bidiyon da ya sake fitarwa , Turji Ya jaddada cewa matawalle na tallafa wa ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso yammacin Najeriya.
Bello Turji ya sake yin bidiyo ne biyo bayan hadiman Bello Matawalle a baya baya-bayan nan sun musanta bayanan na Turjir.
Mai bai wa ministan shawara akan harkokin yada labarai, Deyemi Saka, ya musanta ikirarin Turji, yana mai cewa ba su da tushe balle makama.
Sai dai Turjin a a sabon bidyon nasa ya jaddada bayanansa in da ya ce “Wace riba zai samu dan ya yi wa Matawalle Sharri?”