Dole mu haɗa kai domin magance matsalar tsaro – Shugaban Senegal

Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya yi kira a ranar 19 ga Nuwamba da a ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar soji tsakanin ƙasashen Yammacin Afirka domin tunkarar ƙalubalen da suka haɗa da “ta’addanci” da ƙaruwar safarar haramtattun kayayyaki da rashin zaman lafiya, kamar yadda jaridar L’Observateur mai zaman kanta ta ruwaito a ranar 20 ga Nuwamba.

Ya ce: “Tsaron Yammacin Afirka ba zai iya ci gaba da dogaro da tsarin tsaron kowace ƙasa daban-daban ba. Lokaci ya yi da za a haɗa ƙarfi da ƙarfe tare da amfani da ƙarfi da damar da yankin ke da su.”

Ya kuma buƙaci a ƙara inganta hangen nesa da ƙarfin soji, da musayar bayanan sirri ta hanyoyin da suka dace, tare da gudanar da atisayen hadin gwiwa akai-akai.

Faye ya bayyana hakan ne a babban birnin ƙasar, Dakar, yayin bikin ranar rundunar sojin ƙasar.

Yayin da yake jaddada muhimmancin kare haɗin gwiwar yankin duk da sauye-sauyen siyasa da na hukumomi da ake fuskanta, Faye ya tunatar da irin dogon tarihin da Senegal ke da shi na aiki tare da sojojin ƙasashe abokan hulɗa wajen hana ɓarkewar rikice-rikice da kuma magance su a faɗin yankin.

A cewarsa, irin waɗannan gogewa da aka samu tare za su iya zama ginshiƙi wajen sake gina haɗin gwiwa mai karfi, wanda zai dogara kan zurfafa fahimtar sabbin barazanar tsaro da kuma samar da hanyoyin ɗaukar matakai cikin gaggawa.

Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da manyan hafsoshin sojin kungiyar Ecowas suka gudanar da taro a Dakar domin tattauna hadin gwiwar tsaro, taron da kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar ba su halarta ba, bayan da suka fice daga kungiyar a watan Janairun 2025

Post masu alaƙa

Ruwan sama ya mamaye tantinan ‘yan gudun hijira a Gaza

Aƙalla jiragen fasinja 12 a Turai sun fuskanci tangarɗa

Ɗan takarar shugaban ƙasa da ya sha kaye a zaɓen Brazil ya tsere zuwa Amurka