DAGA: YASIR ADAMU
Sabon Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa ba za a samu sauƙi ko magance yawan satar kuɗaɗen gwamnati a Najeriya ba, har sai an hana ma’aikatan gwamnati samun damar sata suna gina gidaje, da sayen manyan motoci da kuma kai ƴaƴansu makarantu masu tsadar gaske.
Yace tilas a samar da yanayin da dole ma’aikacin gwamnati yana da zaɓi, ko dai ya yi abinda ya dace, ko kuma ya fuskanci hukunci idan ya yi sata.
Shugaban na EFCC Ola Olukoyede ya ce shi ɗan Najeriya wanda ba shi da gidan kansa, da zarar ya samu wata dama, to kuɗi zai sata don ya sayi gidan. Ko da ba shi da damar yin satar, sai ya ƙirƙiri yadda zai saci kuɗin.
Da yake magana kan manyan ɓarayin Najeriya kuwa, Olukoyede ya ce yan kwangila sun sace Naira Tiriliyan 2.9 tsakanin shekarar 2018 zuwa shekarar 2020 a ƙarƙashin gwamnatin Buhari. Ya ce bincike mai zurfi ya yi daga shekarar 2018 zuwa shekarar 2020 a kan wasu mutane da kamfanoni 50. Kuma binciken a kan harƙallar kwangila ce kawai inda ya gano satar da aka yi.
Ya ce waɗannan maƙudan kuɗaɗe da aka sace a waɗannan shekarun da ya yi bincike, sun isa a yi amfani da su wajen yin ayyukan raya ƙasa da gina al’umma. Olukoyede ya bayyana takaici kan yadda ake satar kuɗaɗen Najeriya a ƙarƙashin shugabanni da jagororin da aka ɗora wa hakkin jan ragamar al’umma ko hukumomi da ma’aikatun gwamnati.