DAGA: FATIMA MUHAMMAD
Kungiyar matan ’yan sanda ta Najeriya reshen jihar Kaduna ta gudanar da shirin bayan da tallafin kayan masarufi ga iyalan ’yan sandan da suka rasu yayin da suke tsaka da yaki da hare-haren ’yan ta’adda da kuma rikice-rikicen kabilanci a jihar.
Uwargidan kwamashinan ’yan sandan jihar Kaduna Hajiya Shifa Musa Garba ce ta jagoranci bikin rabar da kayan tallafin kayan masarufin karkashin kungiyar matan ’yan sanda wato Police Women Association POWA.
Uwar gidan kwamashinan ’yan sandan ta jihar Kaduna ta yi kira ga ’yan kasuwa da kungiyoyin bayar da agaji da kamfanoni da su rinka agazawa rayuwar mata da yara marayu da ’yan sandan da suka mutu a fagen fama suka bari.
Hajiya Shifa Musa Garba ta yaba matuka bisa kokarin da wannan kungiya take yi a duk shekara na bayar da agajin rayuwa ga ’ya’yan kungiyar musamman wadanda suka rasa mazajensu.
Malama Lubabatu Umar Wurno ita ce mai magana da yawun wannan kungiya ta POWA reshen jihar Kaduna.
“Da ma ainihin kungiyar an samar da ita ne saboda tallafawa matan ’yan sanda, tana tallafawa mata akasari, sannan kuma tana sauraron matsalolin mata da kuma matsalolin gidajen matan ’yan sanda, to wannan tallafi da ta yi yana daya daga cikin ire-iren abubuwan da kungiyar take yi, daman dai duk shekara muna yi na gaba daya da komai da komai, to wannan kadan daga cikin dan abubuwan da muka saba yi ne sai muka debo mata 100 aka tallafa masu, a baya dai mata 60 ne muka diba, to amma saboda yanayi sai muka samu adadin da ya zartar hakan.”
Matan da suka dace da tallafin sun bayyana matukar jin dadinsu bisa wannan tagomashi.