DSS ta bayyana dalilanta na cigaba da tsare tsohon gwamnan babban banki, Godwin Emefiele

Hukumar tsaro ta farar kaya DSS, ta shaidawa babban kotun tarayya da ke zama a garin Abuja hikimar cigaba da tsare Godwin Emefiele.

Inda ta ce, tsohon Gwamnan na babban bankin kasa na CBN zai tsere daga Najeriya ne muddin aka ba shi beli.

Jami’an tsaro sun bayyana Emefiele a matsayin barazana ta fuskar hawa jirgin sama ya bar Najeriya yayin da ake kokarin cigaba da bincike a kansa.

Post masu alaƙa

Yadda wata tifa ta take mutum 2 a kan babur a Jos

Yan sanda sun kama ’yan bindiga 2, sun ƙwato dabbobi 76 a Katsina

AIG Garba Ahmed ya karrama sabon kwamishinan yan sanda CP Taiwo a Kano.