Yadda wata tifa ta take mutum 2 a kan babur a Jos

Mutum biyu sun rasa rayukansu bayan da wata tifa ta murƙushe babur ɗin haya da suke kai a Mahaɗar Infant Jesus da ke kan titin Rukuba, a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa da ke Jihar Filato.

Da yammacin ranar Laraba ne lamarin ya faru a daidai lokacin da mazauna yankin ke komawa gidajensu bayan kammala harkokin yau da kullum.

Wata ganau mai suna Joy Nankin ta shaida wa wakilinmu cewa direban babur ɗin hayar yana ɗauke da fasinjoji biyu ne lokacin da tifar da ke gudun wuce kima ta buge babur ɗin a mahadar.

Ta ce, “Lamarin ya faru cikin ƙanƙanin lokaci. Direban babur yana ƙoƙarin tsallaka mahadar ne sai tifar ta zo daga baya ta take su.”

Post masu alaƙa

Yan sanda sun kama ’yan bindiga 2, sun ƙwato dabbobi 76 a Katsina

AIG Garba Ahmed ya karrama sabon kwamishinan yan sanda CP Taiwo a Kano.

Yan sandan Kano sun miƙa wa masu su motoci biyu da suka ƙwato tare da kama mutum Daya da ake zargi.