Yan sanda sun kama ’yan bindiga 2, sun ƙwato dabbobi 76 a Katsina

Jami'an Rundunar 'Yan sanda

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, ta daƙile yunƙurin satar shanu, tare da kama wasu mutum biyu da ake zargin ’yan bindiga ne, sannan ta ƙwato dabbobi 76 da aka sace a lokacin wasu hare-hare daban-daban.

’Yan sanda sun ce sun gudanar da ayyukan ne tare da haɗin gwiwar sojoji da kuma jami’an sa–kai na jihar (KSCWC).

A cewar rundunar, wasu ’yan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari ƙauyukan Yarmaje da Alasawa da ke Ƙaramar Hukumar Dutsinma a ranar 24 ga watan Yuli, inda suka sace dabbobi da dama.

Bayan samun rahoton lamarin, jami’an tsaro suka bi sahun maharan har zuwa tsakanin ƙauyukan Faguwa da Garangamawa.

Bayan musayar wuta, ’yan bindigar sun tsere tare da barin dabbobin da suka sace.

Jami’an tsaron sun ƙwato shanu 20 da tumaki 56.

A wani samame da aka gudanar a daren ranar a Ƙaramar Hukumar Musawa, jami’an tsaro sun tare wasu mutum uku.

Ɗaya daga cikinsu, wanda na ɗauke da bindiga ƙirar AK-47, Ind ya buɗe wa jami’an tsaron wuta kafin ya tsere.

Sai dai jami’an sun kama sauran mutane biyun, Babangida Lawal mai shekara 28 da Ismail Lawal mai shekara 25.

Haka kuma, sun ƙwato ƙwanson harsasai biyu na AK-47 a wajen.

A halin yanzu, waɗanda ake zargin suna hannun ’yan sanda, kuma suna taimakawa wajen gudanar da bincike.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Katsina, Ali Umar Fage, ya yaba wa jami’an tsaron bisa jajircewarsu.

Sannan ha jaddada ƙudirin rundunar na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar.

Post masu alaƙa

Yadda wata tifa ta take mutum 2 a kan babur a Jos

AIG Garba Ahmed ya karrama sabon kwamishinan yan sanda CP Taiwo a Kano.

Yan sandan Kano sun miƙa wa masu su motoci biyu da suka ƙwato tare da kama mutum Daya da ake zargi.