DSS ta kama wani matashi da ake zargi da safarar makamai a Kano

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta kama wani mutum mai shekara 30 da haihuwa, Muhammad Abubakar, bisa zargin safarar makamai a Jihar Kano.
DSS ta bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne a ƙaramar hukumar Gezawa bayan samun bayanan sirri, yayin da yake kokarin kai bututun makamin roka guda huɗu (RPG), bindigogi kirar AK-47 guda uku da bindigu biyu marasa harsasai zuwa Funtua a Jihar Katsina.
A cewar hukumar, wanda ake zargin direban sufuri ne, kuma ya amsa cewa ya karɓi makaman daga wani mutum mai suna Bello a yankin Maigatari da ke kan iyakar Jihar Jigawa domin kai su wani yankin da matsalar tsaro ta yi kamari.
Muhammad Abubakar ya ce an yi masa alkawarin biyan sa Naira 450,000 bayan ya isar da kayan, amma jami’an tsaro suka kama shi kafin ya kai ga kammala aikin.
DSS ta ce za ta gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu, yayin da take ci gaba da haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin cafke sauran waɗanda ake zargi da hannu a lamarin

Post masu alaƙa

Kotu ta daure Saminu shekaru 15 kan kisan abokin kasuwancinsa, ta umarce shi da biyan Naira miliyan 10.

Gwamnatin Najeriya ta amince da biyan ma’aikata Naira 70,000 alawus din sufuri

An fitar da matar da ta kai cutar Ebola Najeriya daga ƙasar