Farashin mai ya faɗi sosai saboda hasashen cimma yarjejeniya tsakanin Iran da Amurka

Farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya faɗi sosai cikin kusan watanni huɗu, sakamakon fatan da ake da shi na cewa za a cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran nan ba da jimawa ba.

Farashin danyen mai na Brent ya sauka zuwa dala 87.33 a kowanne ganga, inda ya ragu da dala 3.05, wato kimanin kashi 3.4 cikin ɗari idan aka kwatanta da ranar da ta gabata.

Haka zalika, farashin danyen mai na Amurka ya sauka zuwa dala 84.88 a ganga, ragin dala 2.83, ko kuma kashi 3.2 cikin ɗari kenan.

Wannan shi ne mafi ƙasƙancin farashin danyen mai na Texas cikin kusan watanni uku, tun daga watan Afrilu da ya gabata.

Masu kasuwa na ƙara samun kwarin gwiwa cewa yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran na dab da kammaluwa, abin da ke rage fargabar rikici a yankin Gabas ta Tsakiya.

Wani masani a harkar saka hannun jari, John Kilduff na kamfanin Again Capital, ya ce abin da ya janyo faduwar farashin shi ne bayanan da Iran ta bayar na cewa akwai takardar fahimtar juna da ake shirin kullawa da Amurka, wanda ya sa masu zuba jari ke sa ran samun daidaito a kasuwar mai.

Post masu alaƙa

Ɗan Majalisar Tarayya Yaya Tongo ya rasu

DSS ta kama wani matashi da ake zargi da safarar makamai a Kano

Ɗalibai da malamai da aka sace na cikin gandun dajin Old Oyo – Makinde