Dubun masu ƙera muggan makamai a Filato ta cika

Dubun wasu masu ƙera muggan makamai ta cika a yankin Lantang da ke Jihar Filato mai yawan fama da rikice-rikice da hare-hare.

Sojojin Rundunar Operation Enduring Peace sun kama manyan bindigogi uku, ƙirar AK-47 guda biyu da kuma ƙirar G3 guda ɗaya a hannun masu ƙera makamai ba bisa ka’ida ba.

Mutanen sun shiga hannun sojoji ne a lokacin da dakarun rundunar suka kai samame a masana’antar makaman da ke yankin Gwandanu, da ke ƙaramar hukumar Langtang.

Kakakin rundunar, Kyaftin Polycarp Oteh, ya ce sojojin sun kama mutanen tare da kayan aikinsu ne, a yayin da suke tsaka da aikin ƙera muggan makaman.

Post masu alaƙa

Kotu ta dage hukunci kan shari’ar datse yatsa bisa alkawarin naira miliyan 80.

An Kashe Makiyaya 50 An Sace Shanu Sama da Dubu 2 A Kaduna — MACBAN

Tinubu ya yi alhinin rasuwar Bamanga Tukur