Dalilin da ya sa na gina Masallatai 50 da aurar da marayu 10 — Mataimakin Gwamna

Mataimakin Gwamnan Jihar Yobe, Idi Barde Gubana ya ƙaddamar da masallatai 50, kuma ya tallafa da auren marayu mata 10 da ya rena a ƙaramar hukumar Fune ta jihar.

An gudanar da wannan tallafin ne a ƙarƙashin shirinsa, na Gidauniyar Gorbo wacce ta mayar da hankali kan tallafawa da ilmantar da marayu, mata da sauran ƙungiyoyi masu rauni.

Da yake magana da manema labarai yayin buɗe ɗaya daga cikin masallatan da aka gina a fadar Sarkin Fune, mataimakin gwamnan ya ce an yi wannan shirin ne don kusantar da mutane ga Allah.

Gubana ya bayyana cewa, yana goyon bayan auren marayu mata 10 ga abokan zamansu da suka zaɓa bayan ya rene su da kuma ilmantar da su.

Ya bayyana wannan tallafin a matsayin wani aiki na sadaka da kuma godiya ga Allah da ya ɗauke shi daga matsayinsa na mai tawali’u zuwa matsayin mataimakin gwamna.

“A halin yanzu muna da marayu sama da 1,400 a ƙarƙashin kulawarmu yadda muke horar da su tun daga firamare har zuwa sakandare, kuma wasu yanzu suna cikin manyan makarantu yayin da wasu sun kammala karatunsu sun sami abokan tarayya na aure, shi ya sa muka tallafa wa auren su,” in ji shi.

Don haka ya ƙara yin kira ga masu hali da ‘yan siyasa da su tallafa wa marayu, su gina masallatai, sannan su saka hannun jari a cikin shirye-shiryen da zai zama na taimakawa jama’a musammam masu ƙananan ƙarfi da marayun da ke cikin su.

Da yake jawabi wajen buɗe masallacin babban limamin masallacin ƙasa, Abuja, Farfesa Ibrahim Maƙari ya yaba wa mataimakin gwamnan kan wannan taimako.

Duk da haka, ya roƙe shi da ya ƙara tallafa wa marayun da suka yi aure da jarin farko don taimaka musu su kafa ƙananan kasuwanci a gidajen aurensu.

Post masu alaƙa

Dalilin da ya sa zan yi takara – Yusuf Buhari

An tsinci gawar matashi a kusa Asibitin Mallam Aminu Kano.

Tinubu ya cire ministan kuɗi da na gidaje