• Home  
  • EFCC ta ƙwace gidajen Malami a Abuja
- Babban Labari

EFCC ta ƙwace gidajen Malami a Abuja

Jami’an Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa sun yi wa gidajen tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami ƙawanya a wani yunkuri na ƙwace muhallin tsohon Babban Lauyan na Najeriya. Tun dai a ranar Litinin da ta gabata ce jami’an EFCCn suka ka ziyarci wasu gidajen tsohon ministan da ke Maitama […]

Jami’an Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa sun yi wa gidajen tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami ƙawanya a wani yunkuri na ƙwace muhallin tsohon Babban Lauyan na Najeriya.

Tun dai a ranar Litinin da ta gabata ce jami’an EFCCn suka ka ziyarci wasu gidajen tsohon ministan da ke Maitama a Abuja, da zummar rufe bisa abin da suka bayyana a matsayin aiwatar da umarnin kotu.

Rahotanni sun nuna cewa jami’an EFCC sun je wuraren ne da safiyar ranar, inda suka sanya alamar hattara da haramta amfani da gine-ginen, duk da ƙorafin Malami kan sahihancin umarnin kotun da jami’an suka gabatar.

Malami ya ce umarnin kotun da aka bayar tun a ranar 6 ga Janairu, 2026 na wucin gadi ne na tsawon kwanaki 14 kacal, wanda a cewarsa ya riga ya ƙare, kuma ya ƙalubalanci matakin a gaban kotu.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000