EFCC ta gurfanar da ƴan Indiya a kotu kan zargin zamba cikin aminci

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta gurfanar da wasu ƴan Indiya uku tare da wani ɗan Najeriya a gaban kotun jiha ta Kwara dake Ilorin, ranar Laraba, 17 ga Disamba, 2025.

Ana tuhumarsu ne da laifuka biyu da suka shafi haɗin baki da aikata lafin zamba cikin aminci yayin da suke ma’aikata a Kamfanin KAM Steel tsakanin watan Nuwambar 2024 zuwa Satumba 2025.

Hukumar ce ta sanar da hakan a shafinta na X.

Waɗanda ake tuhuma sun musanta dukkan zargin da ake musu a lokacin da aka karanta musu ƙarar.

Bayan haka, lauyan EFCC, Cosmas Ugwu, ya nemi a tsare su a hannun hukumar gyaran hali har zuwa lokacin shari’a.

Sai dai lauyoyin wadanda ake tuhuma sun nemi a a basu beli saboda laifukan da ake tuhumarsu da shi za su iya neman beli.

Amma kuma lauyan EFCC ya ce wasu daga cikin waɗanda ake tuhuma ‘yan kasar waje ne kuma suna iya tserewa idan har aka sakesu, sannan ya nemi kotu ta hanzarta shari’ar.

Bayan sauraron hujjoji daga bangarorin biyu, Alkalin ƙotun, Sulaiman Akanbi ya ɗage shari’ar zuwa ranar Juma’a, 19 ga Disamba, 2025.

Post masu alaƙa

Dalilin da ya sa na gina Masallatai 50 da aurar da marayu 10 — Mataimakin Gwamna

Dalilin da ya sa zan yi takara – Yusuf Buhari

An tsinci gawar matashi a kusa Asibitin Mallam Aminu Kano.