Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa ɗalibai da malamai da aka sace a karamar hukumar Oriire na jihar har yanzu suna hannun masu garkuwa a cikin gandun dajin Old Oyo National Park.
Ya bayyana hakan ne a sabon bayanin da ya fitar game da ƙoƙarin ceto su, kusan makonni hudu bayan aukuwar lamarin.
Makinde ya ce jami’an tsaro na ci gaba da aiki tukuru domin kubutar da wadanda aka sace a yayin hare-haren da aka kai makarantu a garuruwan Yawota da Ahoro-Esinle a ranar 15 ga watan Mayu, 2026.
A cewarsa, rahotannin sirri sun nuna cewa har yanzu ana tsare da su a cikin babbar gandun dajin Old Oyo, wadda ke da fadin kusan kilomita murabba’i 2,500 a yankuna da dama na jihar.
Ya kara da cewa girma da wahalar shiga yankin na kawo kalubale ga jami’an tsaro, don haka ana bukatar tsari mai kyau da hadin gwiwa domin samun nasarar aikin ceto.
Gwamnan ya tabbatar wa al’umma cewa ana bin duk wata sahihiyar hanya domin ganin an ceto wadanda aka sace ba tare da wata illa ba.
Ya kuma bukaci jama’a da su kasance cikin shiri su kai rahoton duk wani abin da ke da alaka da laifi ta hanyar layin gaggawa na jihar, tare da gargadin cewa yada jita-jita na iya kawo cikas ga aikin ceto