Farashin man fetur ya sake ƙaruwa a rana ta uku a jere a faɗin duniya, sakamakon ƙazantar rikicin da ke tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran, lamarin da ke ƙara fargabar tangarɗar samar da mai.
Yaƙin dai ya haifar da tsaikon haƙar mai da iskar gas a rijiyoyin mai a faɗin yankin Gabas ta Tsakiya da dakatar da jigilar man ta Mashigar Hormuz.v
Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito cewa zuwa ƙarfe 04:00 na safe agogon GMT a ranar Talata, farashin ɗanyen mai na Brent ya kai dala $79.44 kan kowace ganga, bayan ƙarin dala $1.70, wato kashi 2.2 cikin 100.
A ranar Litinin, farashin ya kai dala $82.37, mataki mafi tsada da ya kai tun watan Janairun 2025, kafin daga bisani ya sauko kaɗan amma an rufe kasuwar cinikayyar ɗanyen man da ƙarin kashi 6.7 cikin 100.
Haka kuma, ɗanyen mai na Amurka, West Texas Intermediate (WTI), ya ƙaru da dala $1.17 (kashi 1.6 cikin 100), inda ya kai $72.40 kan kowace ganga, mataki mafi tsada da ya kai tun watan Yuni.
- Ramadan: Gwamna Namadi ya kaddamar da rabon kayan abinci da kudade ga ma’aikatan Jigawa
- Gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri ya koma APC
Sai dai farashin ya ɗan sauko gabanin rufe kasuwar da ƙarin kashi 6.3 cikin 100.
Wani mai nazarin kasuwancin a kamfanin IG, Tony Sycamore, ya ce muddin ba sassauta rikicin cikin gaggawa, ko Mashigar Hormuz ta ci gaba da kasancewa a rufe, kuma Iran ba ta daina kai hari kan cibiyoyin makamashi a yankin Gabas ta Tsakiya, ta babu makawa farashin zai ci gaba da tashi.
“Matuƙar ba a samu sassaucin rikici cikin gaggawa ba, tashin farashin zai ci gaba da ƙaruwa, musamman idan yaƙin ya daɗe yana gudana,” in ji shi.

