Shugaban Hukumar Hisbah dake nan Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce akwai sarƙaƙiya wajen yin fatawa da ta shafi abubuwa masu jibi da kirifto, inda ya ƙara da cewa wannan ne yasa bai fiya ba da fatawa akan kirifto ba don gudun kawo rudani.
Fitaccen malamin addinin musuluncin ya ce lamarin fatawa abu ne da yake buƙatar nutsuwa da kuma lura, don gudun bada fatawa da gurguwar fatawa.
A karatuttukan malamin na baya dai an yi masa tambayoyi akan kirifto, sai dai malamin yana kaucewa amsa tambayar kai tsaye, ko kuma ya bada shawarar a tutunbi wasu malaman da suke da sani a fannin.
Kungiyar Editocin Najeriya Ta Karrama Kwamishinan Yaɗa Labaran JIhar Kano
Ana yawan samun fatawowi masu cin karo da juna tsakanin malamai, inda wasu ke haramta kirifto ɗin kai tsaye, a ɗaya bangaren kuma wasu malaman na ba da goyon baya da ayi.
Sha’anin kirifto na daga cikin manyan abubuwan da kasuwar su ke ci musamman a tsakanin matasa, inda wasu suka riƙi harkar a matsayin