Sifeto Janar na ‘yan sandan kasa, Usman Alkali Baba, ya umarci kwamishinan ‘yan sandan Filato, CP Bartholomew N. Onyeka da ya rufe dukkan manyan ofisoshin kananan hukumomin jihar 17.
Sanarwar mai dauke da sa hannun kakakin rundunar ‘yan sandan Filato DSP Alfred Alabo, ya ce ,matakin ya zama dole biyo bayan zaman dar dar, kan yiwuwar barkewar rikici kan neman shugabancin kananan hukumomin, da kuma barazana ga rayuka, dukiya da kuma sauran ababen more rayuwa.
Rundunar ‘yan sandan ta yi gargadin cewa ba za ta zuba idanu ta kyale bata gari su tayar da zaune tsaye ba, dan haka aka rufe baki dayan manyan ofisoshin kananan hukumomin jihar Filato 17.
Daga karshe kwamishinan, ya yabawa al’ummar jihar Filato bisa yadda suke ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai , inda ya bukaci jama’a su ci gaba da gudanar da sana’o’insu cikin kwannciyar hankali.