Gamayyar kungiyar shugabanni a jihar Ribas sun bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya nada Sanata Magbys Abe a matsayin daya daga cikin ministocinsa.
Majiyarmu ta rewaito cewar, wannan bukatar na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun jagoran kungiyar, Sunnie Chukumele, da sakataren kungiyar, Josiah Onoriode.
Kungiyar dattawan na Ribas sun bayyana cewa za su yi farin ciki da ganin shugaban kasa Tinubu ya zabi Sanata Abe cikin majalisar zartarwa ta tarayya wanda a ke gab da kafawa.
Sanarwar ta ce: “Mun lura cewa an mayar da Sanata Magnus Ngei Abe saniyar ware ko an ture shi gefe a shirye-shiryen al’amuran siyasa a fadar shugaban kasa.
“Mun yarda cewa nada Sanata Abe, a majalisar shugaban kasa Tinubu zai karfafa ainahin wadanda suka yarda da shugaban kasar da mabiyansa na gaskiya a fadin jihar.