Home » Kungiyar kasashen Musulmi na gudanar da taron gaggawa kan kona Alkur’ani a Sweden

Kungiyar kasashen Musulmi na gudanar da taron gaggawa kan kona Alkur’ani a Sweden

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment
Kungiyar kasashen Musulmi na gudanar da taron gaggawa kan kona Alkur'ani a Sweden

Kungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya OIC na gudanar da wani taron gaggawa a birnin Jeddah na ƙasar Saudiya domin nazarin matakin bai ɗaya da za a ɗauka kan ƙona Al’qur’ani mai girma da aka yi a ƙasar Sweden a ranar Laraba.

Ƙasar Saudiyya ce dai ta shirya Tattaunawar wacce za ta nazarci matakan da suka dace a ɗauka kan abin da ƙungiyar ta kira ”abin Allah wadai” da aka aikata.

Tuni dai ƙungiyar ta yi Allah wadai kan abin da matashin ɗan asalin ƙasar Iraki da ke gudun hijira a Sweden ya aikata a wajen babban masallacin Stockholm babban birnin ƙasar Sweden ranar Idin Babbar Sallah.

Dayawan ƙasashen musulmi sun dawoda jakadunsu da ke Sweden gida domin nuna ɓacin ransu da kuma aike wa da saƙon Allah wadai.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?