Kungiyar Matasan Kudu Maso Yammacin ƙasar nan ta bukaci shugaba Bola Ahmad Tinubu da kada ya naɗa wani tsohon gwamna mukamin minista a gwamnatinsa.
Shugaban kungiyar, Kwamared Funsho Ajimuda ne ya bayyana hakan ga manema labarai a cikin wata sanarwa da ya fitar ajiya Asabar. Inda Ya zargi tsoffin gwamnonin da lafta wa jihohinsu basukan na bagaira ba dalili.
Ya ce, “Kamar yadda ake ta yamaɗidin cewar, wasu gwamnoni da dama na ta neman mukaman minista da wasu mukamai. Babu komai a cikin hakan illa tsagoran son kai da son zuciya bayan da suka shafe shekaru takwas a matsayin gwamnoni amma sun bige da neman kujerar minista.
Wannan kungiya na fatan za a yi watsi da wannan bukatar ta tsoffin gwamnonin a matsayin ministoci.