Home » Ghana: An karrama ma’aikatan lafiya 300 da suka yi yaki da cutar kwarona

Ghana: An karrama ma’aikatan lafiya 300 da suka yi yaki da cutar kwarona

by Anas Dansalma
0 comment
Ghana: An karrama ma'aikatan lafiya 300 da suka yi yaki da cutar kwarona

Gwamnatin Ghana ta karrama fiye da ma’aikatan lafiya 300 da suka yi yaki da cutar korona a kasar.

Shirin bayar da lambar yabo, wanda shugaban Ghana Nana Akufo-Ado ya kaddamar, wani yunkuri ne na yaba wa ma’aikatan kiwon lafiya kan gagarumar gudunmawar da suka bayar lokacin da cutar COVID-19 ta barke a kasar.

Kamfanin dillanci labaran na Ghana News Agency ya rawaito cewa, sama da ma’aikatan lafiya 300 daga babban asibitin koyarwa na Tamale ne suka samu wannan lambar yabo ta shugaban kasa a jiya Talata.

Daga cikin ma’aikatan da aka karrama akwai likitoci da nas-nas da ungozoma da masu hada magunguna da jami’an abinci mai gina jiki da ma’aikatan dakin gwaje-gwaje da direbobi da kuma masu aikin wanki na asibitin da masu gyaran wutar lantarki da dai sauransu.

An mika su takardar karramawar ce mai dauke da shaidar sa hannun shugaban kasar Akuffo-Addo.

Kazalika an ba da lambar yabo ga babban asibitin TTH a matsayin wurin da ya nuna juriya da kwazon aiki wajen samar da yanayin da ya dace a lokacin barkewar cutar.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi