Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya rantsar da sabbin kwamishinoni akalla 35 da ya naɗa a matsayin mambobin majalisar zartarwasa.
Sabbin kwamishinonin sun yi rantsuwar kama aiki ne a zauren majalisar zartarwa da ke fadar gwamnatin jihar Ebonyi, inda Gwamnan ya buƙace su da su kawo sabbin abubuwa da dabarun sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.
Haka nan kuma gwamna Nwifuru ya rantsar da shugaban ma’aikatansa, Farfesa Emmanuel Echiegu, da mataimakinsa, Injiniya Timothy Nwachi, da mashawarta na musamman da sauransu.
Da yake jawabi ga waɗanda ya bai wa mukamai, gwamnan ya ce ya naɗa su muƙamai ne ba dan siyasa ba, inda ya roƙesu da su haɗa hannu wuri ɗaya domin kai jihar tudun mun tsira, ya kuma ce gwamnatinsa ba zata lamurci sakarci ba.