Wutar gobara da ta tashi a safiyar Lahadi a sanadin wutar lantarki ta laƙume shaguna 50 a tsohuwar Kasuwar Sakkwato.
Wutar ta kama a layi mafi tsada a kasuwar inda ake sayar da kayan tireda da harkar canjin kuɗi da turare da sauran kayan abinci na kwali, inda ta cinye kayan miliyoyin naira wanda har yanzu ba a ƙididdige kimarsu ba.
Shugaban ƙungiyar ’yan kasuwa na Jihar Sakkwato, Alhaji Cika Sarkin Gishiri, ya ce wutar ta soma ne da misalin ƙarfe 10 na safe a ranar Lahadi ta laƙume shaguna 50 tare da cinye kaya da kuɗinsu zai kai miliyan 100, sai dai ba a samu hasarar rayuwa ba.
Alhaji Sarkin Gishiri ya roƙi gwamnatin jiha ta tallafa wa waɗanda abin ya shafa domin su ci gaba da kasuwancinsu.
- Sojojin Najeriya sun kashe ƴanbindiga fiye da 40 a Borno
- Rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wadanda ake zargi da kashe matar aure da yayan ta 6 a Dorayi.
Gwamnan Sakkwato Ahmed Aliyu ya jajanta wa ’yan kasuwar da suka samu ibtila’in gobarar ya yi alƙawarin gwamnati za ta tallafa wa waɗanda lamarin ya shafa..
Gwamna ya bayyana lamarin matsayin jarabawa daga Allah, kuma y yi kira ga waɗanda shagunansu suka ƙone su bar wa Allah.
“Wannan gobarar ta shafi gwamnati da dukkan al’ummar jiha, ba ta tsaya kawai ga ’yan kasuwa ba,” a cewar Gwamnan.
Ya bayyana cewa kasuwar tana cikin manyan wuraren da ake samar da kayan more rayuwa ga mutanen jiha.

