Gobe Ba Aiki A Kano: Hutun Sabuwar Shekarar Musulunci 1447

Daga : Sharif Khalifa Sharifai

Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana ranar Alhamis, 26 ga Yuni, 2025 a matsayin ranar hutun murnar Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1447 bayan Hijira.

Wannan na cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya fitar a ranar Laraba.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya taya al’ummar Musulmi murnar samun damar ganin sabuwar shekara, wadda ke farawa da watan Muharram – watan farko a kalandar Musulunci.

Ya kuma bukaci jama’a da su yi nazarin abubuwan da suka gabata tare da amfani da wannan dama wajen yin addu’ar neman zaman lafiya, hadin kai da ci gaban Kano da Najeriya gaba ɗaya.

Post masu alaƙa

NDLEA Ta Kama Mutane 1,860, Ta Kwace Ton 5.4 na Miyagun Ƙwayoyi a Kano.

INEC ta bayyana dalilin cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen da ta fitar

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 6 a Adamawa