Gwamantin Jigawa ta raba sababbin motoci da babura domin ƙarfafa sa ido a makarantu

Gwamnatin Jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Umar A. Namadi ta kaddamar da rabon motoci 27 da babura 280 domin ƙarfafa ayyukan sa ido da kula da ingancin koyarwa a makarantun firamare na jihar.
Babban sakataran Ma’aikatar Ilimi na matakin farko ta Jihar, Baffa Abubakar, shi ne ya bayyana haka ga wakilin MUHASA na Jihar Jigawa Ali Rabiu Ali, inda ya ce inganta ilimi ba ya tsaya kan ɗalibai kawai, sai an tallafa wa masu sa ido da kayan aiki.
“Gina ingantaccen ilimi ba ya tsaya ga ɗalibai a aji. Ya haɗa da samar wa masu sa ido abin hawa domin su rika gudanar da aikinsu yadda ya dace,” in ji shi.
Ya ce za a raba baburan guda 280 ga School Support Officers (SSOs), yayin da Education Secretaries za su karɓi sabbin motoci 27 domin sauƙaƙa zirga-zirga da inganta rahotanni daga makarantu.
Ya ƙara da cewa gwamnati za ta ƙara babura a cikin kasafin 2026 domin tabbatar da cewa kowane SSO zai mallaki abin hawa kafin ƙarshen shekarar 2026.
Jigawa ta samu gagarumin ci gaba a karatu da lissafi-PLANE Babban sakataran ya bayyana cewa jihar ta kaddamar da babban shiri tare da New Globe Education Services Limited, wata ƙungiya ta fasahar ilimi da ke aiki a Amurka, Birtaniya, Indiya, Sin da ƙasashen Afirka da dama.
Ya ce Jigawa ce jiha ta farko a Arewacin Najeriya da ke amfani da tsarin, wanda zai inganta koyarwa ta amfani da na’urorin zamani.
A ƙarƙashin yarjejeniyar shekara biyar mai darajar Naira biliyan 63, za a tallafa wa makarantu 1,162 a faɗin jihar.
A cewarsa, bayan tantance bukatun kowace makaranta: Malamai za su sami ƙwasa-kwasan horo na tsawon kwanaki 10, Kowane malami zai samu na’urar kwamfutar hannu mai ɗauke da darussa, Shugabannin makarantu za su karɓi wayoyin zamani domin bibiyar halartar malamai,  ka zalika za a samar da dashboard a Ofishin Gwamna, Majalisar Zartarwa, Ma’aikatar Ilimi da SUBEB domin ganin abin da ke faruwa a makarantu a lokaci guda (real-time).
Ya ce tsarin zai rage yawan rashin halartar malamai da inganta kula da ɗalibai.
“Za ka iya ganin adadin malamai da ɗalibai a aji, da darasin da ake yi a wannan lokaci. Wannan zai inganta ayyukan koyarwa da karatu ƙwarai,” in ji shi.
Abubakar ya yi kira ga iyaye su tabbatar da cewa yaransu suna zuwa makaranta, musamman ganin yadda zamani ke buƙatar haɗa ilimin boko da na addini.
“Idan ka ilmantar da yaro, ka ilmantar da al’umma. Muna da ilimin addini, amma yau ilimin zamani ya zama wajibi domin tafiya da sabon salo,” in ji shi.
Ya tabbatar da cewa gwamnatin Namadi na da ƙudirin canza tarihin ilimi a Jigawa ta hanyar zuba jari da tsare-tsare masu ɗorewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *