Gwamna Bala Abdulkadir Ya Musanta Zargin Shirin Sauya Sheka Daga PDP Zuwa PRP

Gwamnatin Jihar Bauchi, ta ƙaryata zargin cewa Gwamna Bala Mohammed na shirin ficewa daga PDP zuwa jami’yyar PRP.

Jita-jitar ta samo asali ne bayan Sakataren jam’iyyar PRP na Bauchi, Hon. Wada Abdullahi, ya ce ba za su karɓi gwamnan zuwa jami’yyarsu ba.

Ya ce gwamnan bai cika ƙa’idojin da PRP ke buƙata ba a shugabancinsa a Bauchi.

Amma mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin yaɗa labarai, Mukhtar Gidado, ya ce gwamnan bai taɓa tunanin barin PDP ba.

Ya ce babu wata tattaunawa ko mataki da aka ɗauka na komawa PRP.

Gidado, ya ce gwamnan na aiki ne wajen ƙarfafa PDP kuma ya taɓa doke PRP a zaɓuka da suka gabata.

Ya ƙara da cewa Jihar Bauchi ta samu ci gaba a ƙarƙashin gwamnan, musamman a ɓangaren tallafa wa jama’a, ababen more rayuwa, ci gaban ƙauyuka, da yawon buɗe ido.

Gwamnatin ta soki PRP kan yaɗa jita-jita marasa tushe.

Ya ce gwamnan na da ’yancin zaɓar makomarsa a harkokin siyasa, amma duk wata shawara da zai ɗauka ba za ta kasance bisa ƙarya ko jita-jita ba.

Post masu alaƙa

Kotu ta dage hukunci kan shari’ar datse yatsa bisa alkawarin naira miliyan 80.

Ba za mu dawo da tallafin man fetur ba —Fadar Shugaban Ƙasa

An Kashe Makiyaya 50 An Sace Shanu Sama da Dubu 2 A Kaduna — MACBAN