Gwamnan Abia ya ziyarci Tinubu a Villa

Gwamnan jihar Abia, Alex Otti ya ziyarci Shugaba Tinubu a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja.

Duk da cewa babu cikakken bayani game da ziyarar, wasu a ƙasar na ganin ba ta rasa nasaba da batun shugaban ƙungiyar ƴan awaren Biafra, Nnamdi Kanu da aka yanke wa hukuncin ɗaurin rai-da rai cikin watan da ya gabata.

A baya-bayan nan ne jaridun ƙasar suka ruwaito cewa gwamnan Abia ya kai ziyara da jagoran Biafran a gidan yarin Sokoto da yake ɗaure.

A lokacin ziyarar zuwa Villa, gwamnan Abin na tare da ƙanin Nnamdi Kanun, Emmanuel Kanu da kwamishinan shari’ar jihar, Ikechukwu Uwanna (SAN) da wasu jami’an gwamnatin jihar, kamar yada gidan Talbijin na Channels ya ruwaito.

Post masu alaƙa

Sojojin Najeriya sun daƙile yunƙurin garkuwa da mutane tare da ceto mutum 23

Dan KAROTA da direba ya buge ya gudu Nasiru Abdullahi Mai Jihadi ya rasu ya bar mata 2 da ‘ya’ya 12.

An kama budurwa ‘yar shekara 15 kan safarar miyagun kwayoyi a Delta.