Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kai ziyara wasu yankunan jihar da ke fama da hare-haren ƴanbindiga.
Yayin da yake jawabi a ƙauyen Kamaye na ƙaramar hukumar Tsanyawa, gwamnan ya nuna takaicinsa kan yadda ya ce ƴanbindiga daga Katsina ke tsallakawa jihar domin ƙaddamar da hare-hare da sace mutane.
”Abin takaici ne yadda ƴanbindiga za su yi sulhu a Katsina amma su tsallako mana Kano su riƙa kashe mana mutane da sace wasu”.
Gwamnan wanda ke tare da manyan jami’an tsaron jihar ya nemi haɗin kan al’ummar yankin wajen bai wa jami’an tsaro bayanan sirri domin magance matsalar.
”Ina kira gare ku, ku saka idanu tare da bai wa jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar ba su bayanan sirri kan ƴanbindigar da zarar kun samu labarin zuwansu”, in ji Abba Kabir Yusuf.
Gwamnan ya kuma jajanta wa al’ummar yankin kan kashe-kashen da ƴanbindigar suka yi tare da sace wasu a yankunan.