Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana shirinsa na sauya sheka zuwa Jam’iyyar ADC, inda ya ce jam’iyyar na da damar kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2027.
Idan Bala Mohammed ya sauya shekar, ADC ta samu gwamna mai ci na farko, wanda hakan zai kara mata karfi a kan tsofaffin gwamnoni da tsofaffin ministoci da sauransu da suke cikinta.
Bala Mohammed ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan taron sirri da ya yi da tawagar shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa, ƙarƙashin jagorancin tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal, a Bauchi.
Mohammed ya ce shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa, Sanata David Mark, ya gayyace shi da magoya bayansa zuwa jam’iyyar, yana bayyana ADC a matsayin “mafakar da aka fi so.”
Sai dai ya jaddada cewa tattaunawa da shawara na ci gaba domin tabbatar da yanke hukunci mai kyau.
A cewarsa, jam’iyyarsa ta PDP ta zama “ba ta da shugaba,” kuma ƙoƙarin sasanta rikice-rikicen cikin gida ya gaza, lamarin da ya sa magoya bayansa ke matsa masa lamba ya duba wasu wuraren.
Ya ce: “Mun tsinci kanmu cikin mawuyacin hali inda jam’iyyarmu ba ta da shugaba. Dole mu nemo mafaka a cikin jam’iyyun adawa. ADC ta bayyana a matsayin dandalin da ya fi ɗorewa da karbuwa a wurin jama’a.”
Gwamnan ya jaddada cewa ba zai yi wannan shawara da sauƙi ba, amma tsarin jam’iyyar da shugabancinta sun sa ta zama zaɓi mai jan hankali. Ya kuma bayyana cewa an kafa kwamitoci biyu—ɗaya a Abuja da ɗaya a Bauchi—domin tantance hanyar siyasa da za su bi, ciki har da binciken zabi a cikin jam’iyyun adawa daban-daban.
A cewarsa, ci gaba da zama cikin yanayin siyasa da ba a so su ba ba zai yiwu ba, don haka akwai buƙatar haɗuwa da dandalin adawa mai ƙarfi.
Tun da farko, jagoran tawagar ADC, Babachir David Lawal, ya ce ziyarar ta fito ne daga shugaban jam’iyyar na ƙasa domin gayyatar gwamna Bala Mohammed ya shiga ADC kafin zaben 2027.
Babachir Lawal ya bayyana gwamnan a matsayin ɗan siyasa mai ƙarfin hali wanda shigarsa jam’iyyar zai ƙara mata ƙarfi. Ya kuma jaddada muhimmancin haɗin kan jam’iyyun adawa, yana gargadin cewa rashin haɗin kai na iya haifar da mummunan sakamako ga makomar Najeriya.
Taron ya zo ne kwanaki kaɗan bayan gwamna Bala ya kira taron masu ruwa da tsaki na PDP a Bauchi domin tattauna makomar jam’iyyar a jihar, ciki har da yiwuwar ci gaba da zama a PDP ko kuma sauya sheka.
Majiyoyi sun bayyana cewa taron na cikin shirin kammala sauya shekar gwamnan da dukkanin tsarin PDP a jihar tare da wasu zababbun jami’ai zuwa ADC