Gawuna ya koma ADC a hukumance, ya yi rajista a matakin mazaba.

Tsohon mataimakin gwamnan Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, ya koma jam’iyyar ADC a hukumance, inda ya kammala rajista tare da karɓar katin zama ɗan jam’iyya a mazabarsa ta Gawuna da ke ƙaramar hukumar Nasarawa a jihar.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Gawuna ya je yin rajistar tare da jagoran tafiyar Kwankwasiyya kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, wanda shi ma ya yi rajista a matsayin ɗan jam’iyyar ADC a ranar Litinin.

Wannan mataki ya biyo bayan sanarwar da Gawuna ya yi ta ficewa daga jam’iyyar APC a ranar Litinin, lamarin da ke nuna sauyi mai muhimmanci a tafiyarsa ta siyasa.
A yayin rajistar, magoya baya da manyan jiga-jigan jam’iyya sun hallara domin shaida wannan lamari tare da nuna goyon bayansu ga tsohon ɗan takarar gwamna na APC a zaɓen 2023.
Taron ya kasance mai cike da jama’a, inda aka ga yadda magoya baya suka fito domin nuna farin ciki da goyon baya ga sabon matakin da Gawuna ya ɗauka.

Post masu alaƙa

Ƴan bindiga sun sace tsohon mai magana da yawun soji a Katsina

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta rushe tsagin APC mai goyon bayan Wike a Ribas

Sojojin Najeriya sun ceto mutum 31 da aka sace a Zamfara